Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 222 Da Duniyan Nan da Girmanta da Yawan Daɗin Rai Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 222 Da Duniyan Nan da Girmanta da Yawan Daɗin Rai Lyrics

Hymn 222 Da Duniyan Nan da Girmanta da Yawan Daɗin Rai Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 222 Da Duniyan Nan da Girmanta da Yawan Daɗin Rai Lyrics

 

1
Da duniyan nan da girmanta da yawan daɗin rai
Su dā sun jarabce ni, sun kama ni sosai.
Amma da dukan daɗinsu ban ƙoshi ba daɗai,
Gama raina ba ya ƙoshi in ban da kai kaɗai.
Yesu, Yesu, Yesu Gurasar Rai,
Ban yarda ba, ban yarda ba a raba ni da kai.

2
Ko raina ya matsu fa, ko kewa na ke ji,
Ko ina shan wahala, ko ciwo na ke yi,
Ni sai in nemi Yesu, shi ne ya ce in zo,
In faɗa masa duka, in roƙi taimako.
Yesu, Yesu, Yesu Mai Taimako,
Ban yarda ba, ban yarda ba a raba ni da kai.

3
Alkawarin Mai Cetonmu ba za ya tashi ba.
Mai zuwa ba a ƙinsa in ya zo da gaskiya.
Ina dalilin zafin zuciya, babu hutawa?
Ga Yesu yana jira, ba iyakar tausayi.
Yesu, Yesu, Yesu mai ƙaunata,
Ban yarda ba, ban yarda ba a raba ni da kai.

Post navigation

Previous: Hymn 188 Dā Ina Zaune Cikin Duhuna Lyrics
Next: Hymn 394 Cikin Gidan Uban Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version