Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 22 Da Yamman Nan, Ya Yesunmu Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 22 Da Yamman Nan, Ya Yesunmu Lyrics

Hymn 22 Da Yamman Nan, Ya Yesunmu Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 22 Da Yamman Nan, Ya Yesunmu Lyrics

 

1
Da yamman nan, ya Yesunmu,
Albarkaci maganarka,
Haskaka, Yesu, duhunmu
Bishe mu kuwa da Ruhunka.
Ya Yesunmu, mai taimako,
Ƙarfafa ranmu duka yau.
Ya Yesunmu, mai taimako,
Ƙarfafa ranmu duka yau.

2
Magaucinmu ya bi mu yau.
Da wayonsa, ya ruɗe mu.
Jaraba ma mai zafi ce,
Halinmu kuwa rarrauna ne.
Ya Yesunmu, mai nasara,
Ka cika mu da Ruhunka.
Ya Yesunmu, mai nasara,
Ka cika mu da Ruhunka.

3
Laifofinmu dayawa ne,
Tunaninmu miyagu ne,
Harshenmu duk da gurinmu,
Sun ƙara mana laifinmu.
Ya Yesunmu, yafe mu dai,
Da jininka, ka wanke mu .
Ya Yesunmu, yafe mu dai,
Da jininka, ka wanke mu.

4
Ya Ubangiji, Allahnmu,
Ka tsare mu da daren nan,
Da hannunka ka riƙe mu,
Da ikonka, ƙarfafa mu.
Ya Yesunmu, ka keƃe mu,
Har safiya, ka tsare mu.
Ya Yesunmu, ka keƃe mu,
Har safiya, ka tsare mu.

Post navigation

Previous: Hymn 399 Dan Ina Bin Hanyar Zunubi Lyrics
Next: Hymn 396 Da Hannuna Biyu Zan Yi Aikinka Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version