Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 65 Don Jibin Nan, Mai Fansarmu Lyrics
1
Don jibin nan, Mai Fansarmu,
Gurasarka da ƙoƙonka,
Ƙaunarka da alherinka,
Mun gode maka, Yesunmu.
2
Kai ne ka ɗauke laifinmu,
Ka wanke mu da jininka,
Kai ne ka zama gurbinmu,
Mun gode maka, Yesunmu.
3
Domin ka ɗauki giciyenka,
Ka kuma raina kunyarsa
Domin ka ba da jininka,
Mun gode maka, Yesunmu.
4
Domin ka aiko Ruhunka,
Shi koya mana nufinka,
Shi buɗe mana kalmarka,
Mun gode maka, Yesunmu.
5
Domin alkawarinka fa
Na shirin zaman masu bi
Har za ka zo ka karƃe mu,
Mun gode maka, Yesunmu.