Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 412 Ga Mu Nan Shehuna Gabas Lyrics
1
Ga mu nan shehuna gabas
Mun kawo maka sujada,
Daga nesa mun yi murna
Da ganin tamraruwa.
KORUS
Ga tarmamuwa, can sama,
Tarmamuwa haskaka
Cikin zukatanmu duka
Har mu cika nufinsa.
2
Mun kawo maka dukiya,
Ga zinariya-zumuntarmu
Kai ne sarki, yi ta mulkinka
Cikin zukatanmu.
3
Ku mutane yau kun taru,
Kuna murna tare da mu.
Ko kun san wanda an haifa,
Ko shi ne naka ceto.