Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 428 Jaraba Ta Shaiɗan, Ƙi Yarda da Shi Lyrics
Jaraba ta Shaiɗan, ƙi yarda da shi
Kowace nasara za ta ƙarfafa ka.
Yi yaƙi ba fashi, ƙi tsohon mutum
Ka zan duba ga Yesu, Shi zai kai ka gaba.
KORUS
Roƙi taimakon Yesu
Ҡarfin hali, nasara
Shi zai riƙe hannunka
Shi zai kai ka gaba.