Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 204 Ka Bishe Ni, Ya Jehovah Lyrics
1
Ka bishe ni, ya Jehovah,
Ni baƙo ne a duniyan nan.
Ni rarrauna, kai Mai Iko,
Riƙe ni da hannunka.
Ka cishe ni, ka cishe ni,
Da gutasan nan mai rai.
Da gurasan nan mai rai.
2
Buɗe mini, ya Mai Ceto,
Maƃulƃula masu rai.
Ka bishe ni da idonka,
Har an kai ni a wurinka,
Taimakona, taimakona,
Kai ka zama ƙarfina.
Kai ka zama ƙarfina.
3
In na taka kwarin mutuwa,
Kau da dukan tsorona,
Tokare ni da hannunka,
Kai ni can a gidanka.
Waƙar yabo, waƙar yabo
Taka ce har abada.
Taka ce har abada.