Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 464 Mai Tsarki Lyrics
KORUS
Mai tsarki, mai tsarki, Allah mai tsarki
Ubangiji karɓi sujadarmu
Allah mai tsarki.
1
Mala’iku na sama suna rairawa
Suna cewa kai ne mai tsarki
Allah mai tsarki.
Korus
2
Ƴaƴenka sun taru domin sujada
Muna roƙo ka tsarkake mu
Don kai ne mai tsarki.
Korus
3
Mutanenka mun taru domin raira yabo
Muna cewa kai ne mai tsarki
Allah mai tsarki.
Korus
4
Dukan halittu na duniya masu lumfashi
Mu ɗaukaka Allah mai tsarki
Ubangijinmu.
Korus