Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 174 Na Ji Kiranka Yanzu, Ya Ubangijina Lyrics
1
Na ji kiranka yanzu, ya Ubangijina.
A cikin jininka, Yesu, ka wanke zuciyata.
KORUS
Ubangijina, ga ni nan, na zo,
Sai ka ji addu’ata, ka ba ni taimako.
2
Ko na zo da zunubi, da rashin ƙarfina,
Na sani kai ba za ka ƙi ka tsarkake ni ba.
Korus
3
A wurinka kaɗai akwai murna sosai.
Kai ne ka ba ni kwanciyar rai da sanin gaskiya.
Korus
4
Ina so in ci gaba, in zama cikakke,
In koyi irin halinka, in ɗauki giciye.
Korus