Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 187 Na Sami Ceto Ta Wurin Yesu Lyrics
1
Na sami ceto ta wurin Yesu.
Shi ne Ɗan Ragon da Allah ya bayar
Domin ya mutu saboda mu,
Mu sami pansarmu wurinsa.
KORUS
Ceto na Allah kyauta ne
Ceto na Allah kyauta ne.
Yesu Mai Ceto,
Alhamdu ga Allah,
I, Ceto na Allah kyauta ne.
2
Na yi ƙoƙari in sami ceto
Cikin ayyukan da jiki ke yi,
Ni dai na kasa, duk banza ne.
Ai, ceto na Allah kyauta ne.
Korus
3
Ran da na tuba na sami ceto,
Yesu ya yafe duk zunubaina,
Na sami rai na har abada,
Bukata ta biya, an cece ni.
Korus
4
Duk ƴanuwana, ku zo wurinsa,
Yau sai ku tuba, ku karƃi Yesu,
Bar neman ceto gun ayyuka
Don ceto na Allah kyauta ne.
Korus