Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 319 Rayukan Duk Jama’a A Gabanka Su Ke Lyrics
1
Rayukan duk jama’a a gabanka su ke,
Mutanen dukan zamanu, kowace halitta. Harsunan dukan duniya, yamma da gabas kuwa,
Gare ka su ke rerawa, Maɗaukaki ne kai.
2
Ga wanda mu ke ƙauna, Mai Cetonmu ne shi,
Sunansa yana goshinmu, suna mai tsarki.
Shi ne kaɗai da iko, mai kā da mutuwa,
Yesu na Nazarat a dā, Allah har abada.
3
Mu ma a wannan duniya, a tsakiyar yaƙinmu,
Mun karƃi iko wurinka, Yesu Shugabanmu.
Mu dai mun ji kiranka, ba za mu fasa ba.
Ƴan yaƙi nan, mu huta can, hutu madauwami.