Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 210 Sai Ku Nemi Shawara Gun Yesu Fa Lyrics
1
Sai ku nemi shawara gun Yesu fa.
Kome ya same ku nan a duniya,
Sai ku shaida masa, ku ji nufinsa.
Yesu ne mai shawararmu dai.
KORUS
Yesu Kristi
Shi zai taimake mu cikin dukan kome.
Yesu Kristi
Shi ne mai taimakon mu Masu Bi.
2
Ko mun fāɗa cikin tarkon jaraba,
Sai mu nemi ƙarfafawa wurinsa.
Ko mun yi tuntuƃe har da faɗuwa,
Sai mu nemi gafara tun yau.
Korus
3
Ko mun fāɗa cikin ƙuncin tsanani,
Sai mu nemi ƙarfi wurin Mai Ceto
Muna so mu zama masu shaidarsa,
Kada mu yi musun sunansa.
Korus