Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 76 Tashi, Mu Gai da Ubangijinmu Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 76 Tashi, Mu Gai da Ubangijinmu Lyrics

Hymn 76 Tashi, Mu Gai da Ubangijinmu Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 76 Tashi, Mu Gai da Ubangijinmu Lyrics

 

1
Tashi, mu gai da Ubangijinmu.
Yau aka haife shi da safen nan.
Mai Ceton duniya, Ubangiji ne.
Ya zo ya ɗauki siffar ɗan Adam.
Tashi, mu ji waƙar mala’iku,
Ƙaunar Ubangiji ne zancensu.

2
Yabo ga Allahnmu Maɗaukaki,
In ji su taron rundunan Sama.
An kawo muku yau da daren nan,
Bisharar murna zuwa duniya duk.
A birnin Dawuda aka haife shi,
Mai Ceto, shi ne Almasihunku.

3
Da jin labari, makiyayan nan
Sai suka tashi za su wurinsa.
A Baitalahmi, ga jaririn nan
A kwance dai cikin sakarkari.
Sun tashi kuwa, sun ba da shaidarsu
Manzannin farko ne na Ɗan Mutum.

4
Mu kuwa da halin ladabi mu ji
Labarin haihuwarsa ta ƙanƙanci.
Tuna da haifuwarsa da giciyen,
Bi sawun Yesunmu da hawaye.
Wannan jariri shi ne Ɗan Allah,
Ya kau da dukan hakkin zunubi.

5
Cetattu fa ta wurin ƙaunarsa,
A gaban kursiyi za mu rusuna.
Za mu ga iyakar darajarsa,
Za ya bayyana mana ikonsa.
An haife shi ta wurin budurwa,
Gare shi za mu yi godiya tutur.

Post navigation

Previous: Hymn 526 Ubangiji Shina Ta Biɗa Lyrics
Next: Hymn 272 Ta da Ido, Ka Duba Gonaki Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version