Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 17 Tun Farkon Hasken Safe Lyrics
1
Tun farkon hasken safe
Zuciya ta ke yin yabo ga Yesunmu!
Ko cikin aiki ne, ko wurin wasa ne,
Yabo ga Yesunmu!
2
Ko dare ne ko rana,
Koyaushe sai mu yi yabo ga Yesunmu!
In fa Shaiɗan ya zo, Yesu ‘na taimako
Yabo ga Yesunmu!
3
Ga Allah cikin Sama,
Mala’ikunsa ‘na yin yabo ga Yesunmu!
Mu mutanen duniya, kada dai mu fasa
Yabo ga Yesunmu!
4
Yanzu da ranmu duka
Mu ce da ƙarfinmu, yabo ga Yesunmu!
Tun daga duniya, har can cikin Sama,
Yabo ga Yesunmu!