Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 165 Wa Ke Da Iko Ya Ceci Duniya? Lyrics
1
Wa ke da iko ya ceci duniya?
Ba mutum, ba mutum.
Wa ke da ƙauna ya ba da ransa?
Ba mutum, ba mutum.
Yesu Kristi ya ƙaunace mu,
Shi kaɗai ya ji tausayinmu.
Wa za ya ƙi ba da gaskiya gare shi?
Ba mutum, ba mutum.
2
Wa ya ke so ya yi musun ransa?
Dukanmu, dukanmu.
Wa za ya yarda ya ƙi son kansa?
Dukanmu, dukanmu.
Mu ne nasa, mun ƙi bin wani.
Har ya komo, mu jira shi.
Sauran abu mu maishe su wofi,
Dukanmu, dukanmu.