Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 203 Ya Allahnmu Na Bethel, Kai Mai Jin Addu’armu Lyrics
1
Ya Allahnmu na Bethel, kai mai jin addu’armu,
Yakub a cikin jeji dā, ka biya bukatarsa.
2
Addu’armu da roƙonmu, mun kawo su yanzu.
Ya Allahn ubanninmu, kai ka zama Allahnmu.
3
A cikin dukan ƙuncinmu, ka bi da ƙafarmu.
Abincin yini ba mu dai, ka rufa jikinmu.
4
Ka tsare mu, ya Allahnmu, a cikin duniyan nan.
Har ran da za ka kira mu, mu shiga Sama can.