Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 252 Ya Ubanmu, Sa Albarka Lyrics
1
Ya Ubanmu, sa albarka
Bisa kan ƴaƴanka yau.
Za mu yi yabon sunanka,
Addu’a kuma za mu yi.
Mun ji labarin Ubangiji
Na gaskiya da alheri.
Cikin hasken Almasihu
Za mu gane ƙaunarka.
2
Maganarka ta koya mana
Mu ƙaunaci ƴanuwa,
Mu girmama gaskiyarka,
Mu yi haƙuri kullum,
Mu hori kanmu da aniya
Domin mu yi aikin kirki,
Loton shiru ko na faɗi,
Koyaushe sai kamewa.
3
Bari ruhohinmu duka
Su yi yabon ikonka.
Murna, ƙauna da salama
Su kasance wurinmu duk.
Mu zama amintattu naka,
Ko cikin aiki ko tunani.
Tsakaninmu da ƴanuwanmu,
Mu yi duk domin Yesu.
4
Mu ɗaukaka sunan Allah,
Mu ambaci duk tsarkinsa.
Albarka kuwa ga Almasihu
Da Ruhunsa Mai Tsarki.
Ga Allah Uba, Allah Ɗa kuwa,
Allah Ruhu Mai Tsarki,
Mu ha ka dukan daraja ma,
Allahnmu har abada.