Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 553 Ya Yesunmu, Ka Ba Mu Ruhunka Lyrics
1
Ya Yesunmu, ka ba mu Ruhunka
Ku dattiɓai ku aikinsa,
Ku samari ku yi ta shelarsa
Wanda ya bi Yesu, tsira za ya yi,
Muna murna har yau zu mu yi
Alleluya, Amin, Alleluya, Amin,
Alleluya, Amin.
2
Yesu yana zuwa, za ya karɓe mu.
Abin da ka shibka, za ka girbe shi
Idan ka yanke rumbuna, za ka kai
Zinariya ce, ko azurfa ce, ko itace ne
Ko ciyawa ce,
Mmm, babban kuka, rana ta hume ka.
Mmm, ka ji kumya, rana ta hume ka.
3
Ku masu bi, Almasihu
Ku duba kwatamci,
Akan budurwai, goma,
Biyar, masu azanci
Suna cewa, ina ango?
Ni ban san ku ba, in ji Yesu,
Ni ban san ku ba, ku rabu da ni
Ni ban san ku ba, in ji Yesu.
Halleluya, Amin, Halleluya, Amin
Halleluya Amin.