Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 280 Ƴan Yaƙin Almasihu, Ku Sa Sulkenku Fa Lyrics
1
Ƴan yaƙin Almasihu, ku sa sulkenku fa,
Ku ɗauki kayan yaƙinsa, ku kafa dagarku.
2
Cike da Ruhunsa, da ƙarfi za ku tsaya
Idan kun dubi Almasihu, za ku ci gaba dai.
3
Ku zare takobi, Maganar Allah ce.
Kuma ku ɗauki garkuwarku, wato bangaskiya ce.
4
Karƙashin tutarsa kada ku ji tsoro.
Ku fāda wa maƙiyanku, Shaiɗan da zunubi.
5
Da haka za ku tsaya, kome kashedinsu.
Magauta za su ba ku baya, kome dai ikonsu.